Sakamakon wannan batun ginin katangar tasa dangataka tsakanin Mexico da Amurka tayi rauni, kwanaki hudu kacal da kama aikin Mr. Trump. Tun a jiya Alhamis ne dai sakataren yada labarai na Fadar ta White House, Sean Spicer ya fada wa manema labarai cewa shugaba Trump zai sa harajin kashi 20 ga dukkan wasu kayayyakin da za’a shigo dasu Amurka daga kasar ta Mexico.
Yace wannan sabon harajin zai samar da a kalla dala biliyan 10 a duk shekara cikin sauki da za’a yi anfani dasu wajen gina wannan katangar.
Kakakin yace tuni shugaba Trump ya tattauna wannan batu da shugabannin majilisun dokokin kasar, kuma wannan ne ma yasa yake son sa wannan batu cikin garambawul ga tsarin haraji na Amurka da majalisar zata yi aiki a kai.
Amma daga bisani Fadar ta White tace wannanyana daya daga cikin hanyoyi daban daban da gwamnati take nazari a kansu kan yadda za’a biya kudin aikin katangar. Sai kuma har wayau Fadar ta White House tace shugaba Trump bai yanke shawarar yadda Amurka zata mayar da kudin aikin ba.
Sai abinda ya fito fili shine kudin harajin Amurkawa ne za’a yi anfani dashi wajen ginin wannan katangar wanda ake sa ran ya lakume kudi har dalar Amurka biliyan 15.
Amma kuma abinda ba a sani ba shine ko wane martani ne Mexico zata mayar kan wannan haraji idan hakan ya sami amincewa akan shigo da kayayyaki Amurka daga Mexico yana da muhimmancin gaske ga tattalin arzikin kasar.