Shugaba Trump Ya Jadada Niyar Tsare Kan Iyaka

Wadansu masu zanga zangar goyon bayan bakin haure

Shugaban Amurka Donald Trump ya jadada cewa zai bada fifiko wajen kare kan iyakokin kasar jiya Jumma’a, bayan shafe mako guda ana cecekuce a kan batun bakin haure da ya dauke hankalin ‘yan siyasa a Washington. Ranar alhamis shugaba Trump ya sauya tsarinsa na raba kananan yara da iyayensu, sai dai gwamnatin tana fuskantar babbar kalubalar yadda zata hada iyalai wuri daya ta kuma nemi hanyar tsare su.

Trump ya gana da dangin wadanda suka rasa kanatattunsu a hannun bakin haure.

Yace, Basu Magana a kan asarar rayuka da kuma barna da mutanen da bai kamata su kasance a nan ba suke haifarwa, mutanen da zasu ci gaba da keta doka suka aikata ba daidai ba.

Sabine Durden ta bayyana jimamin rashin danta Dominic. Tace "Na zo nan tare da dana, abinda ya rage min ke nan nashi, tokarsa. Ina taraya tokarshi a makubcin sarka. Ta haka nake rungumar dana".

Cecekucen da aka rika yi wannan makon kan batun shige da fice, yana iya zama babban abinda zai dauke hankali a zaben ‘yan majalisa na rabin wa’adi da za a gudanar a watan Nuwamba, da zai shafi jam’iyar da zata yi rinjaye a majalisa