Shugaban Amurka, Donald Trump ya harzuka kasashen duniya da gayattar da yayi wa shugaban kasar Philippines, Rodrigo Duterte, wanda wasu ke wa kallon shugaban da bai mutunta hakkokin ‘yan kasar shi.
WASHINGTON D.C —
To amma da yake maida murtani ga wannan gaiyattar, kakakin fadar White House, Sean Spicer, yace wannan wata dabara ce gwamnatin Amurka, ta samu ta neman hanyar aiki da shugabannin nahiyar ta Asia, don a taru a maida Koriya ta Arewa saniyar ware.
Ko bayan shugaban na Philippines, shugaba Trump, ya gayyato shugabannin kasashen Thailand da Singapore, da su ziyarci fadarsa ta White House, dake nan birnin Washington.
Sai dai kuma wasu masu fada a Amurka, kamar Dan majalisar dattawa Sen. Chris Coons (D-Delaware) suna caccakar shugaba Trump, kan gayattar shugabannin da ake ganin masu cin mutuncin mutanensu ne, kamar shi shugaba Duterte na Philippines, da ake zargi da alhakin hallaka dubban mutanen kasar sa.