Jami’an ‘Yan sanda sunce basu san yadda mamallakin wadannan nakiyoyi yayi niyyar amfani da su ba musanman ta ganin yadda aka sami nakiyoyin a cikin kusan kowanne daki a gidan.
An kira ‘Yan sanda gidan ne sakamakon wata ‘Yar hayaniya ta cikin gidan.
An tuhumi Pasquale Criscio ranar Alhamis da laifin mallaka da kuma ajiye makamashi tare da hada nakiyoyi ba kan ka’ida ba. Mallakar Nakiyoyin da aka haramnta da kuma laifuka guda biyu na saka kananan yara cikin hadari. A lokacin da ‘Yan sanda suka isa gidan sun tarar da yara kanana da suka hada da Mai kimanin shekaru 15 da kuma Shekara 6 a cikin gidan.
Jami’an ‘Yan sandan sun kara da cewa sinadaran da aka samu a gidan sunyi kama da irin wadanda aka yi amfani dasu a harin da aka kai yayin tseren famfaleke Boston a wata shekara inda wasu wa da kani suka shirya bamabamai.
Babban jami’in Yan sanda John Alston ya fadawa jaridar New Haven Register cewa yawan nakiyoyin da aka samu da sinadaran da ke cikin gida da bakar hodar harsashi “ da wani abu ya faru to da gaba dayan Unguwar da duk wadanda suke ciki da lokaci ya kure musu.”
Facebook Forum