Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Kudu Tayi Watsi da Kiran Ta Biya Kudin Garkuwa daga Makami Mai Linzami


Wasu 'yan Koriya ta Kudu masu adawa da gina garkuwa daga makami mai linzami da Amurka ke ginawa a kasar
Wasu 'yan Koriya ta Kudu masu adawa da gina garkuwa daga makami mai linzami da Amurka ke ginawa a kasar

Gwamnatin kasar Koriya ta Kudu tayi watsi da kiran da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi na cewa sai ita Koriya ta Kudun ta biya Dalar Amurka Biliyan Daya akan Garkuwar makami mai linzami na THAAD.

Ma’aikatar tsaron kasar ce ta ta fitare da sanarawr a yau jumma’a da yak e cewa “Babu wani sauyi tsakanin yarjejeniyar da aka kulla dake tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka cewa gwamnatin Koriya ta Kudu zata bada wuri da kuma kayan aiki yayin da Amurka zata dauki nauyin kudaden da za’a kashe wajen Kafa Garkuwar ta THAAD tare da gyara da gudanar da shirin.”

An cimma yarjejeniyar Girke Garkuwar ta makami mai linzami na Amurka a lokacin mulkin tsohon shugaban kasr Amurka Barack Obama da kuma tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun –hye (pron: Gen-hey). Park tayi nasarar barin kafa garkuwar ya faru da ‘Yan majalisar ta ne ta hanyar tabbatar musu da cewa babu wani Karin kudi da za’a kashe yayin girke Garkuwar.

Amma a yayin wata ganawa da shugaban kasar Amurka yayi da kamfanin dillancin labarai na Reuters a Washington yace yana son Koriya ta Kudu ta biya kudin Garkuwar.

Wani tsohon jami’in ma’aikatar tsaron Amurka yace abinda za’a kashe a kafa garkuwar ya kai kimaini Dalar Amurka Biliyan daya da digo biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG