Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki alkalin nan na jahar California, wanda ya toshe yunkurin gwamnati na dakatar da shirin nan na kare dubban bakin haure daga kora, wadanda su ka shigo kasar ba bisa ka’ida ba tun su na yara.
“Wannan al’amarin na nuna wa kowa yadda tsarin shari’a ya lalace, ta yadda babu adalci ma ciki” abin da Trump ya rubuta Kenan a kafar twitter jiya Laraba.
Wannan caccakar da Trump ya yi, ya auna ta ne kan wani Alkalin a jahar California mai suna William Alsup, wanda ya yanke shar’ar da ta goyi bayan wasu mutane da kuma cibiyoyi, ciki har da Jami’ar California, wadanda suka kai karar gwamnati da zummar dakatar da yinkurin kawo karshen shirin nan na jinkirta daukar mataki kan shirin bada kariya ga yaran da aka kawo Amurka ba bisa ka’ida ba (DACA a takaice). Shirin ya na kare matasa bakin haure wajen 800,000 daga kora.
Alkalin ya yanke hukuncin cewa shirin kariyan ya cigaba da aiki har sai an yanke hukunci kan kararrakin da aka kai.