Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Soki Lamirin Umurnin Shugaba Donald Trump


Belarus - US president Donald Trump, Czech Republic president Milos Zeman, combo
Belarus - US president Donald Trump, Czech Republic president Milos Zeman, combo

Kotun daukaka kara na nan Amurka tace umurnin hana wasu kasashe wadanda galibin su musulmai shigowa nan Amurka umurni ne da yafi karfin sa

Babban kotun daukaka kara ta nan Amurka ta soki lamirin umurnin shugaba Trump

Kotun tace umurnin hana wasu kasahen 6 wadanda yawancin su musulmai ne da shugaba Trump ya hana shigowa Amurka wannan ya wuce karfin ikon sa.

Sai dai kotun tace zata dakatar da nata matsayin tukunna har sai abinda babban kotun kasa tace.

wannan yana nufin umurnin zaici gaba da aiki har sai abinda babban kotu kasa ta yanke hukunci akai.

A farkon wannan watan ne dai umurnin na shugaba Trump ya fara aiki.

Amma tun wani lokaci can baya da yasa wa wannan umurnin hannu a cikin watan farko na wannan shekarar mai karewa.

Wannan batu ya jima yana kai komo har na kusan shekara guda.

Wannan batu da gwamnatin ta Trump ta bullo dashi yayi karo da cikas tun tashin farko, wanda gwamnatin tace tayi ne da miyyar inganta tsaro.

Masu sukan wannan umurnin ne suka maka gwamnati kotu domin dakatar da wannan yunkuri suka ce wannan son kai ne kuma ana neman a takura wa musulmai ne.

Umurnin dai ya hana yan kasashe kamar su Chadi,Iran,Libya,Somalia da Yememn shigowa Amurka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG