Kafofin yada labaren Koriya ta kudu sun bayyana cewa maiyiwuwa taron koli tsakanin shugaba Donald Trump da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai kasance a wata mai zuwa a kasar Singapore.
Jaridar Chosun Ibo da kafar yada labaran Yonhap sun fada tare da kin bayyana majiyoyin su, cewa Amurka da Koriya ta Arewa sun yarda cewa taron zai kasance a cikin sati na uku a na watan Yuni domin gujewa cin karo da taron manyan kasashe duniya bakwai wato G-7 wanda za a yi a kasar CANADA a ranakun 8 da 9 na watan Yuni wanda kuma shugaban na Amurka zai halarta.
Trump ya shaida wa manema labarai a ranar jumma’a cewa bangarorin biyu na da rana da kuma wurin haduwar tasu. A baya ne dai ya ce yankin da babu soji dake tsakanin kasashen Koriya biyu zai iya zama wuri mai kyau domin ganawar tasu.