Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rouhani Ya Ce Kada Amurka Ta Janye Daga Yarjejeniya 2015


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya fada jiya Lahadi cewa, idan Amurka ta janye daga yarjejeniyar da kasar ta kull da manyan kasashen duniya, hukumomin Amurka a Washington za su yi da-na-sani.

A jwabinda ta talabijin, shugaba Rouhani yace, "Idan Amurka ta fita daga wannan yarjejeniyar, ba da jumawa ba za su yi cizon yatsa irin wadda ba su taba yi ko gani ba a tarihi.


Shugaban Amurka Donald Trump, yace daga yanzu zuwa 12 ga wannan wata zai yanke shawara ko ya janye Washington daga daidaiton, ko kuma ya ci gaba da mutunta ta.


Ministan harkokin wajen Farisan, Mohamed Javad Zarif, ya fada ranar Alhamis cewa, Iran, ba zata sake yin wata shawara dangane da yarjejeniyar data kulla da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015 kan shirin Nukiliyar tan ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG