Shugaban Kasar Ruwanda Ya Yi Jawabi Masu Sosa Zujiya A Taron Kwamitin Huldar Kasar

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya yaba da huldar Isira'ila da Rwanda jiya Lahadi, a wani taron Kwamitin Hulda da Jama'a na kungiyar Isira'ila da Amurka (AIPAC a takaice).

Shi ne Shugaban Afirka na farko da ya taba yin jawabi a taron wannan kungiya mai goyon bayan Isira'ila, taron da ya hada dubban 'yan raji da kwararru da kuma 'yan siyasa.

"Jawabina na yau mai sauki ne, Kasar Rwanda, ko shakka babu kawar Isira'ila ce," a cewar Kagame, wanda ake danganta shi da kawo karshen kisan kiyashin da aka yi a kasarsa a shekarar 1994.

Da ya juyo ga kisan kiyashin da aka yi ma Yahudawa a Turai a yayin yakin duniya na biyu, sai ya gaya ma taron da ya hada wakilai wajen dubu 18, cewa irin tarihi mai ban takaicin da kasashe biyun ke da shi, shi ya dada sa Isira'ila da Rwanda su ka kusanci juna.