Shugaba Obama Zai Hau Kujerar Naki Game Da Saudi Arabiya

Shugaban Amurka Barack Obama zai hau kujerar naki ranar juma’a akan dokar da zata bada dama ga wadanda suka tsira, da kuma dangin wadanda suka mutu, kusan mutane 3000 a harin ta'addancin ranar 11 ga watan Satumbar 2001, kai karar gwamnatin kasar Saudi Arabia domin neman diyya.

Obama ya bayyana wannan doka zata saka Amurkawa dake kasahen waje cikin hadari a hukumance. Ana tsammanin 'yan majalisa za su ketare kujerar nakin Shugaba Obama.

Amma sai sun sami kuri’a kaso biyu bisa uku na 'yan majalisar. Riyadh ta bayyana rashin hannu cikin wannan aika-aika mafi muni ta ta’addanci a Amurka. Duk da haka, mutane 15 cikin 19 da suka jagoranci jiragen fasinjoji hudu don kai hari a Birnin New York da Washington, 'yan kasar Saudiyya ne.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito ganin wata wasika daga wasu manyan Amurka suka sanya wa hannu. Cikinsu har da tsohon Sakataren tsaro William Cohen, da tsohon shugaban Hukumar CIA Chief Michael Morell, da tsohon mai ba wa tsohon shugaban Amurka George W Bush shawara akan harkokin tsaro Stephen Hadley.

A cikin wasikar sun yi gargadi cewa dokar za ta cutar da ra’ayin gwamnatin Amurka. Amma 'yan uwan mamatan da wadanda suka tsira na ta kamfen ganin tabbatar da wannan doka.