Shugaba Obama Ya Yaba da Yadda Afirka Ta Yaki Cutar Ebola

Shugaban Amurka, Obama (tsakiya) da shugabannin Liberiya da Guinea kasashe biyu da suka yi fama da cutar ebola

Duk da yabawar da ya yi akan yadda Afirka ta yaki cutar ebola, shugaba Obama ya gargadi kasashen duniya kada su yi sake.

Shugaba Obama ya yaba kwarai da gaske akan abinda ya kira babban ci gaba na yaki da cutar ebola da akayi a wasu kasashen Afirka ta yamma

Sai dai kuma ya gargadi kasashen duniya da kar su yi sake har saii sunga an kakkabe cutar gaba daya.

Shugaba Obama yana Magana jiya sailin da yake ganawa da wasu shugabanni Africa ta Yamma su 3 sailin da suke Magana akan wannan cutar da taso zama alkakai ga yankin na Africa.

Irin nasarar da kasar Guinea,Liberia da Saliyo suka samu tare da taimakon kasar Amurka ya agaza wajen yakar cutar da tayi dalilin kashemutane dubu 10 a yankin amma yau adadin ya ragu da adadin mutane 40 ne kawai ke dauke da cutar a kasar Guneea da Saliyo, yayin da Liberia bata da ko mutum daya dake dauke da cutar a halin yanzu.

Da yake ganawa da shugabannin kasashen ukku shugaba Obama ya yaba da irin kokarin da suka nuna tare da daukar dawainiyar wadanda suka rayu sakamakon wannan cutar.