Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Na Nazarin Cire Cuba daga Kungiyar Kasashen 'Yan Ta'ada


Shugaba Obama
Shugaba Obama

Yayin da yake ziyara a kasar Jamaica shugaban Amurka yace kasarsa na nazarin cire suna Cuba daga jerin kasashen dake ta'adanci

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana jiya Alhamis cewa, nan ba da dadewa ba zai tsaida shawara kan ko zai cire kasar Cuba daga jerin kasashen da Amurka ta dauka a matsayin wandanda ke goyon bayan ayyukan ta’addanci.

Shugaba Obama ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai Jamaica. Yace ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kammala nazarin ayyukan Cuba a kasashen duniya, kuma yana jiran shawarwarin da mataimakansa zasu gabatar.

Saneta Ben Cardin daga jihar Maryland, wani jigo a jam’iyar Democrat a kwamitin hulda da kasashen ketare na majalisar dattijai, ya bada tabbacin cewa, kwamitin ya bada shawarar cire Cuba daga jerin kasashen. Yace,“Amurka tana da kyakkyawar damar bude sabon babi.”

Shugaban Amurkan ya dade yana nuna niyarshi ta cire kasar wadda tsibiri ce, daga jerin kasashen da ake maida saniyar ware, a yunkurin daidaita huldar diplomasiya tsakanin kasashen biyu. Bara shugaban ya sanar da yin hakan bayan raba gari da suka yi na tsawon shekaru hamsin. Sauran kasashe uku da ke jerin kasashen da Amurka ke zargi da goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasashen duniya sun hada da Syria da Iran da kuma Sudan.

XS
SM
MD
LG