Shugaba Obama ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2013

Shugaba Barack Obama, yayinda yake magana akan kasafi kudin shekara ta 2013, daya gabatarwa Majalisar Dokokin Amirka.

Shugaba Barack Obama na Amirka ya gabatar da shawarar karawa masu hannu da shuni da kuma manyan kamfanoni ko masana'antu haraji, tare kuma da rage shirye shiryen gwamnati da dama. Shugaban ya gabatar da wannan shawarar ce a lokacin da ya gabatar da kasafin kudi shekara ta 2013 ga Majalisar Dokokin Amirka.

Shugaba Barack Obama na Amirka ya gabatar da shawarar karawa masu hannu da shuni da manyan kamfanoni da masana'antu harajin da suke biya. Haka kuma ya bada shawarar zaftare shirye shiryen gwamnati da dama. Shugaban ya gabatar da wannan shawara ce a yayinda ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2013 ga Majalisar Dokokin Amirka.

Shugaban yayi wannan jawabi ne a wata jami'a kusa da nan birnin Washington DC, inda ya jaddada bukatar dake akwai na kara kudin da ake kashewa akan harkokin illimi domin dalibai sun samu kwarewar ta farni fasahohi da ake bukata domin samun aiki mai kyau,.

Yace kasafin kudin kusan dala triliyan hudu daya gabatar, ya gabatar ne da nufin karawa tattalin arziki karsashi na gajeren lokaci da kuma rage gibin kasafi kudin gwamnatin taraiyar da wajen dala triliyan hudu cikin shekaru goma masu zuwa. Haka kuma ya gabatar da shawarar karawa masu hannu da shuni da kuma manyan kamfanoni harajin da suke biya da wajen dala triliyan daya da rabi cikin shekaru goma masu zuwa da kuma rage kudin da gwamnatin taraiya ke kashewa.

Wannan kasasfin kudin daya gabatar zai fara aikin ne daga watan okotoba idan Allah ya kaimu, wata daya kafin ayi zaben shugaban kasa dana yan Majalisa. Tilas sai Majalisar dokoki tayi na'am da wannan kasafin kudi kafin ta zama doka. kuma yan jam'iyar Republican ta masu hamaiya da kaukasan harshe suka caccaki abubuwan da kasafin kudin ya baiwa fifiko.