Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Kano

Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Kano

Shugaban Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki jihar Kano, tare da ya bude tashar fiton kayayyaki ta nesa da teku da kuma sabuwar tashar samar da lantarki mai amfani da albarkatun ruwa da gwamnatin Kano ta gina.

Tun a shekara ta 2003 ne aka fara yunkurin tabbatar da wannan tashar fiton kayayyaki ta nesa da teku mai suna Dala Inland Dry Port.

Gwamnatin jihar Kano ce ta samar da filin mai fadin hecta 35, tashar fiton kayayyakin ta Dala ta fuskanci kalubale da dama cikin wadannan shekaru 20 da suka shude kafin ta wanzu, a cewar Alhaji Ahamd Rabiu, manajan Daraktan tashar.

Wani jirgin fadar shugaban kasa samfarin Choper ne ya sauka da shugaba Buhari da mukaraaban sa a filiin tashar dake gefen yamma da birnin Kano, da misalin karfe goma sha daya safiyar litinin din nan. Sai dai shugaban bai ce uffan ba gabani da kuma bayan ya bude tashar a hukumance.

Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Kano

To amma Engr Mu’azu Jaji Sambo, dake zaman ministan sufurin Najeriya ya ce bude tashar wani gagarumin ci gaba ne ga ‘yan Najeriya, musamman mutanen jihar Kano da jihohi makwafta, da-ma kasashe irin su Jamhuriyar Nijar.

A nasa bangaren, Alhaji Usman Dakin gari, babban konturolan hukumar kwastam mai kula da shiyyar Kano, ya ce yanzu Jami’an sa za su rinka aikin tantance kayayyakin da ‘yan kasuwa su shigo da su cikin gida ko kuma wadanda za’a fitar zuwa ketare, kamar yadda suka saba yi a tashoshin fiton kayayyaki na bakin ruwa. Sai dai yace zuwan tashar ta Dala Inland Dry Port ba zai hana jami’an sa ci gaba da cafke masu fasa kwaurin kayayyaki ba akan manyan hanyoyin mota na kasar.

Bayan tashar fiton kayayyaki ta nesa da teku, Shugaba Buhari ya bude tashar samar da lantarki mai karfin megawatts guda 10 da za ta rinka amfani da albarkatun ruwa, sai babbar gadar sama akan titin zuwa Maiduguri da cibiyar koyar da matasa sana’o’i da kuma babbar cibiyar adana muhimman bayanai ta hanyar fasahar zamani, da dukkanin su gwamnatin jihar Kano ta gina akan miliyoyin naira.

Kazalika, shugaban ya kai ziyarar ban girma ga fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Kano - 3'30"