A jawabin shugaba Mohammdu Buhari ya nuna irin matakan da Najeriya ke dauka na yaki da matsalolin dumamar yanayi da kuma muhalli, tare da nuna fagen da yake ganin kasashen duniya zasu iya taimakawa Najeriya.
Baban jami’in hulda da jama’a na fadar gwamnatin Najeriya, Mallam Garba Shehu, yace Buhari ya nuna goyon bayan da gwamnatin kasar ke yi kan dakatar da dumamar yanayi wanda illarta ta fito fili. Idan aka duba yawan ruwan da ya rage a tafkin Chadi baifi kashi goma cikin dari na ruwan da ake dashi a baya ba.
Kafewar tafkin Chadi yayi sanadiyar rasa ayyukanyi ga kimanin mutane Miliyan biyar, wadanda ke sana’ar Noma da kamun kifi. Hakan dai ya taka rawa wajen zuwan kungiyar Boko Haram da samun goyon baya a yankin.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5