Manufar wannan ranar ita ce al'ummomi su inganta zamantakewarsu da abokan zamansu musamman a wuraren da aka samu tashintashina tsakanin kabilu da addinai daban daban.
Saboda wannan ranar Muryar Amurka ta leka jihar Nasarawa, jihar da ta sha fama da tashintashinan kabilanci da addini a watannin baya domin ganin yadda al'ummomin jihar ke cudanya da juna yanzu.
Onarebul Usman Ofo shugaban kabilar Eggon a jihar yace a matsayinsa na shugaba sun zauna da Fulani da kuma sarakunan jihar sun tattauna kuma an samu zaman lafiya. Tun bayan tattaunawar basu sake samu wata rigima ba tsakaninsu.
Shi ma Alhaji Muhammad Useini shugaban Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa yace su kam sun samu zaman lafiya a jihar. Yace yanzu babu wani tashin hankali tsakaninsu da kabilun da suke makwaftaka da juna. Ya kira da su yi biki na raye-raye saboda zaman lafiyan da suka samu.
Masu ruwa da tsaki a jihar su ma sun tofa albarkacin bakinsu. Tsohon gwamnan jihar Sanata Abdullahi Adamu yace kullum burinsu ne a kara samun hadin kai da karfafa dankon zumunci tsakanin al'ummomin jihar. Yace jihar tana da kabilu fiye da talatin. Suna son a samu kauna inda kowa yana ganin shi danuwan kowa ne.
Shi kuwa Sanata Wali Jibrin daya daga cikin masu fada a ji a jihar yace shi yana cikin duk wani abun da zai kawowa jihar cigaba. Yace ba zai yadda yayi anfani da addini ko kabilanci a jihar ba. Ya kira 'yan siyasa cewa idan an zo batun cigaban jihar da samun zaman lafiya a manta da banbancin siyasa.
Shi ma gwamnan jihar Alhaji Umaru Tanko Al-Makura ya jaddada batun zaman lafiya domin samun cigaba a jihar. Yace rigingimun da suka samu can baya sun sa yanzu al'ummomin jihar sun fahimta cewa cigaban jihar ya ta'allaka ne akan samun zaman lafiya. Duk da banbancin addini ko kabila dole ne a sa zaman lafiya gaba.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.