Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Sayi Jiragen Yaki Daga Kasar Amurka


Jiragen yaki na A-29 Super Tucano
Jiragen yaki na A-29 Super Tucano

Amurka zata sayarwa Najeriya wasu jiragen yaki na zamani guda Goma sha Biyu don kawo karshen kungiyar Boko Haram.

A kwanan nan ma’aikatar tsaron Amurka zata sanar da Majalisar Dokokin kasar kudurinta na sayarwa da Najeriya jiragen yaki na zamani har 12, da ake yiwa lakani da A-29 Super Tucano. Kasashen biyu na fatan idan akayi amfani da wadannan jiragen na zamani, fafatawar da Najeriya ke yi da Boko Haram na iya zuwa karshe.

Masu tsara manofufi a Amurka na fatan tabbatar wannan kuduri. Tsohon kwamandan sama Ahmed Tijjani Baba Gamawa, yace tun daga farkon Boko Haram an rasa rayuka da dukiyoyi da kuma kudaden kasa da akayi almundahana da sunan Boko Haram. Ganin iriin shugabancin da ake da shi a Najeriya idan har wannan magana ta tabbata abu ne mai kyau.

Su dai irin wadannan jirage na A-29 Super Rucano, suna hade da makamai da kayan yaki a cikinsu da kuma kayan gyara, farashinsu ya haura Dalar Amurka Miliyan 500. Wato kamar rabin kasafin kudin tsaron Najeriya na wannan shekara kenan, ko kuma ce kamar ninki biyu na albashin gaba daya sojojin Najeriya.

A cewar masanin tattalin arziki Abubakar Ali, duk da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a halin yanzu, akwai bukatar sayan irin wadannan jiragen yaki. Kasancewar idan babu kwanciyar hankali babu sauran jin dadin komai a kasa.

A baya dai Amurka na jan kafa wajen sayarwa da Najeriya kayan yaki sakamakon zargin sojan Najeriya da danne hakkin bil Adama. Jiragen yaki na A-29 Super Tucano irinsu ne kasar Columbia tayi amfani da su wajen tarwatsa ‘yan tawayen FARC, haka kuma kasar Brazil tayi amfani da su wajen fuskantar masu hada hadar miyagun kwayoyi.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG