Tun watan Fabrairu na wannan shekarar tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya canza sheka daga APC zuwa PDP.
WASHINGTON, DC —
Jam'iyyar PDP a karkashin jagorancin shugaban kasa Jonathan da shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Adamu Muazu zasu halarci gangamin karbar tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau zuwa PDP yau Litinin.
Tsohon gwamnan shi ya fara tallatar da jam'iyyar PDP inda ya yi shelar cewa 'yan jam'iyyar ANPP kwansu da kwarkwatarsu sun koma jam'iyyar PDP. Tsohon gwamnan ya shiga jam'iyyar tun watan Fabrairu amma ba'a yi taron gangamin tarbansa a hukumance ba.
Tun a makon jiya shugabanni da sauran magabata da magoya bayan jam'iyyar su kai ta kai komo domin shirya gangamin. Alhaji Musa Dan Birni daya daga cikin wadanda suka shirya taron yace basu dauki gangamin da wasa ba. Yace karbar Ibrahim Shekarau tsohon gwamnan Kano kuma sardaunan Kano ba wasa ba ne a wurinsu kuma ba wasa ba ne a wurin shugabancin jam'iyyar.
Ta fuskar tsaro, jami'an tsaro sun ce sun dauki duk matakan da suka cancanta su dauka domin tabbatar da tsaro. AC Rabilu Uba Ringim kakakin shiya ta daya ta rundunar 'yan sandan Najeriya wadda ta kunshi jihohin Kano, Katsina da Jigawa yace shugabansu na shiyar ya tattara duk wadanda suke da ruwa da tsaki ta harkar tsaro a Kano kowanne an fadakar da shi irin gudunmawar da zai kawo. Zasu tabbatar da tsaro a Kano domin shugaban kasa ya zo lafiya ya kuma koma lafiya.
Ga rahoton Mahmud Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5