Ambassador Danjuma Sheni babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ya rasa aikinsa saboda takaddamar diflomasiya da ya haddasa tsakanin kasar da Afirka ta Kudu.
Ambassador Sheni ya bada umurnin janye jakadan Najeriya na Afirka ta Kudu daga kasar saboda kyamar 'yan kasashen Afirka da wasu tsirarun kasar Afirka ta Kudu suka yi inda suka kashe wasu suka kuma wawure kaddarorinsu. Ambassador Danjuma Sheni ya yi gaban kansa ne ba tare da tuntubar shugaban kasa ba.
Shugaban kasa ya nuna damuwarsa akan irin matakin da Mr Sheni ya dauka ba tare da izininsa ba lamarin da ya janyo cacar baki tsakaninsa da shugaban kasar Afirka ta Kudun. Bugu da kari Sheni ya dauki matakin ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen biyu ke tattaunawa da junansu akan abubuwan dake faruwa a kasar ta Afirka ta Kudu domin kawo karshensu.
Ministar Labaru Patricia Akwashiki ta yi bayani akan matakin da shugaban kasa ya dauka. Tunda shugaban kasa ne ya tura jakadodin kasar zuwa kasashen duniya to duk wanda za'a janye dole ya kasance da sanisa da kuma yaddarsa ba wai ya ji a kafofin labaran talibijan da radiyo ba kamar yadda ya faru da jakadan kasar na Afirka ta Kudu.
Matakin da Sheni ya dauka ya kawo damuwa tsakanin shugabannin biyu, wato tsakanin Jonathan da Zuma.
Tsohon Jakadan Najeria Ambassador Jibrin Tinade yace kowane shugaban kasa shi ne ministan harkokin wajen kasarsa. Duk abun da ma'aikatar harkokin waje zata yi da sunan shugaban kasa ne saboda haka dole ya sani ba wai ya ji a waje ba.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5