Shugaba Joe Biden Ya Ce Ba Zai Dage Takunkumin Tattalin Arziki Akan Iran Ba

Biden

Biden ya ce Amurka na da burin ta koma kan teburin tattaunawa akan makaman nukiliya da Iran, wadda tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi watsi da shi, ya fitar da Amurka.

Amma da aka tambaye shi kai tsaye yayin wata hira da gidan talabijin na CBS, a jiya Lahadi, ko Amurka zata dage takunkumin don maido da Iran kan teburin tattaunawa, sai Biden ya ce “a’a.”

Ayatollah Ali Khamenei

Ita dai wannan yarjejeniya, ta ba Iran damar bunkasa ayyukan sarrafa uranium da kashi 3.6, Amma a tsakiyar 2019, kasar ta koma bunkasa shi da kashi 4.5, sannan a watan da ya gabata ta koma kashi 20 – wanda hakan wani mataki ne da ta cimma tun ma kafin ta shiga yarjejeniyar.

Yayin wata hira da aka yi da shi ta kafar talbijin, shugaban addini, Ayatollah Ali Khameni, ya ce idan Amurka tana so “Iran ta koma kan alkawuran da ta yi, dole sai a dage duk takunkuman da ke aiki.”