Shugaba Goodluck Jonathan ya karbi rahoton kwamitin taron kasa da aka kamala bayan tsawon wata biyar.
A cikin jawabinsa, shugaba Jonathan yace taron ya yi nasara ba kamar yadda wadansu suke tunani tun farko cewa zai zama sanadin kara banbancin ra'ayi da zaman doya da manja tsakanin shiyoyin kasar ba.
A cikin hira da sashen Hausa wadansu da suka halarci taron sun bayyana cewa, ko babu komi sun sami yin sababbin abokai tare da kara fahimtar juna. Daya daga cikin mahalarta taron Aminu Waziri ya bayyanawa wakilinmu Nasiru Adamu el-Hikaya cewa, akwai mutane da dama da yanzu suka saba da su wadanda bai taba sani ba sai a wurin taron. Ya kuma hakikanta cewa sauran mahalarta taron suma sun kulla irin wannan abokantakar da yace zata kara masu fahimtar juna. Yace wannan kuma ya sassauta irin yadda suke kallo da fahimtar juna.
Mahalarta taron da kuma 'yan Najeriya da dama sun jadada kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki rahoton da muhimmanci ta kuma aiwatar da shawarwarin da aka bayar domin ci gaban kasa.
Ga cikakken rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5