Ranar Alhamis shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya shirya kuma ya jagoranci kaddamar da gidauniyar taimakon wadanda bala'in ta'addancin Boko Haram ya rutsa da su.
A yayin kaddamar da gidauniyar an tara kudade kusan Naira Miliyan Dubu Sittin.
A kan wannan shiri na kaddamar da gidauniyar tallafawa wadanda ta'addanci ya kassara a Najeriya, Grace Alheri Abdu ta tattauna da Hajiya Hafsat Ahmed Marshal, marubuciya, 'yar gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, wadda ta furta albarkacin bakin ta kamar haka:
Daidaikun mutane da kungiyoyi ne su ka bayar da gudunmowa baicin gwamnatin tarayyar Najeriya da ta zubawa gidauniyar Naira miliyan dubu 10.
Ana kyautata cewa za a yi amfani da kudaden wajen sake tsugunar da wadanda bala'in ta'addanci ya tarwatsa a duk fadin kasar Najeriya tare da farfado mu su da hanyoyin yin rayuwar su ta yau da kullum.
Mutane fiye da dubu goma sha uku ne suka hallaka cikin hare-haren 'yan Boko Haram a yayin da wasu dubban daruruwa suka bar wuraren su, kuma dubban kadarori da dukiyoyin jama'a suka salwanta.