Shugaba Erdogan Na Turkiya Na Huskantar Matsala A Zaben Yau

Shugaban Turkiya, Erdogan

A yau Lahadi ne ‘yan kasar Turkiyar suke gadanar da zabe a fadin kasar. Ana sa ran shugaban Turkiya kasar Recep Tayyip Erdogan yana huskantar matsala a wannan zaben kuma akwai yiwuwar zai rashi tasiri mayna biranen Ankara da Istanbul.

Yayin da tattalin arzikin kasar ke huskantar matsaloli da kuma tsadar rayuwa, damuwa a kan tattalin arzikin kasar itace babbar batu dake cikin hankalin masu kada kuri’a.

Tattalin arzikin mu na kara tabarbarewa saboda mulkin da rashin iya aikin su, inji Erdem wani injiniya, wanda ya yi magana kafin ya kada kuri’arsa a Istanbul, yana cewa, abokai na da dama suna nema aikin yi wasu kuma sun rasa ayyukan su saboda tabarbarewar tattalin arziki.

Istanbul shine babban birni mafi girma a Turkiya kuma babban birnin hadadadr kasar. A cewar wani kuri’ar jin ra’ayin jama'a, za a yi kankankan a zaben. Jami’iyar AKP ta Erdogan ta kwashe sama da shekaru 15 tana tasiri a birnin Istanbul.

Wani mai kada kuri’a yace akwai abubuwa masu inganci da za a gani a wannan zaben, yace zasu yi nasara da babbar rata, inji Sinan dan jami’iyar AKP mai mulki bayan ya jefa kuri’arsa.