Shugaba Donald Trump Yana Cigaba Da Sukar Masu Bincikensa

Shugaba Donald Trump

A jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya sake sabunta caccakar da yake yi akan binciken tsige shi, kwanaki biyu kafin a fara sauraron bahasi a bainar jama’a da ake zargin yayi amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba domin ya taimaki kansa a siyasance.

Kafin a fara bikin ranar tsoffin sojoji ta shekara shekara don girmama sojojin Amurka a bikin da aka gudanar a birnin New York, shugaba Trump ya wallafa wani zargi a shafinsa na Twitter, ba tare da ya bada wata hujja ba, yana cewa dan majalisa Adam Schiff, jagoran da ke kula da binciken tsige shi a majalisar wakilai, ya yi karin gishiri a bayanan jami’ai takwas wadanda suka bada shaida a cikin ‘yan makonni nan da suka gabata ba’a bainar jama’a ba a cikin wani killataccen daki a ginin majalisar wakilan Amurka da ke Capitol Hill.

A cewar rubutattun bayanan, jami’an diflomasiyyar da suke aiki da wadanda suka yi ritaya da kuma jami’ai masu kula da tsaron kasa sun yi bayani dalla-dalla yadda shugaba Trump da hadimansa suka takurawa Ukraine ta kaddamar da bincike kan daya daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar Demokrat da ke kan gaba wajan shirin kalubalantar sa a zaben shekarar 2020, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da aikin dansa Hunter Bidens a kamfanin makamashi na Ukraine da kuma wani hasashen da ake karyata cewa, Ukraine ce, ba Rasha ba, ta yi katsalandan a zaben shekara 2016, kamar yadda gamayyar jami’an tsaron Amurka suka ce.