Shugaba Donald Trump Bai Fito Karara Ya Soki Shirin Kasar Isra'ila Na Ci Gaba Da Gine Gine A Gabar Tekun Jodan Ba

Majalisar tsaro ta kasar Izraila, ta amince da samar da matsugunnin yahudawa na farko a yammacin kogin Jordan a cikin shekaru 25, yayin da yanzu haka tana ci gabada tattaunawa da Amurka akan mataki na gaba.

Gidajen Yahudawa da aka gina a yammacin kogin Jordan, tun a shekarar 1992 an fadada wadanda aka gina ne a wani lokaci can baya. Sai dai wadannan da aka amince a gina su a jiya kusa da Shillo, zasu zama rukuni na farko da za a gina sabbi fil.

Firayin Ministan kasar Benjamin Neteyanhu, yayi alkawarin samar wa daruruwan mutanen da aka tilasta musu barin matsugunnan su na Amona, wanda babbar kotu tace an gina su a inda bai dace, ba domin ko an gina su ne a filin Falesdinawa, abinda yasa aka rushe su.

Su dai wadannan sabbin da za a gina, za a samar dasu ne a kusa da na farko dake yammacin gabar kogin Jordan, inda Falesdinawa ke fatar ganin ya zame musu babbar hedikwatar sabuwar jiha.

Sai da Falesdinawa, na kallon samar da wadannan gine-ginen da Izraela ke son yi a matsayin abinda zai kawo wa zaman lafiya tsakani al'ummun biyu cikas.

Sau tari majalisar dinkin duniya tana kallon wannan yunkurin samar da matsugunni da Izraila ke son tayi a matsayinm abinda ya saba, kuma bai dace ba. Sai dai Shugaba Trump, bai bi sahun Shugaba Obama ba na fitowa nan da nan ya soki lamirin wannan manufa ta Izraila.