Ma'aikatar shari’ar Amurka, ta gurfanar da ita gaban alkali amma Candace Marie Clairbone, tace bata yarda tana da laifi ba.
Ita dai Claiborne kwararra ce a sashen sarrafa harkokin ofis na ma'aikatar harkokin wajen Amurka, kuma tun a shekarar 1999 take rike da wannan mukamin.
Tana rike da mukamin harkokin tsaro na shiga da fitar da bayanan sirri a manya da kananan ofisoshin jakadancin Bagadaza,Khartoun,Shanghai, da kuma Beijin.
Masu gabatar da kara suna tuhumar Claiborne ne da kabar dubban daloli da wasu kyaututtuka da suka hada da kumfutar tafi da gidanka, da ciyar da ita, da kuma biya mata kudin wasu tafiye-tafiyen da tayi, har da kyautar gida.
Har wayau masu gabatar da karar suka ce, jami'an leken asirin na kasar China sun bukaci Claborne ta basu bayanan sirri akan taron harkokin tattalin arzikin Amurka da China, su kuma su bata kudi.
Yanzu haka daya daga cikin manyan laifuffukan da ake tuhumar ta da aikatawa sun hada da kin fada wa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, wato FBI dangantakar ta da wakilan kasar China.
Jami'an ma'aikatar shari'ar Amurka, sun ce Claborne, tayi anfani da mukamin da take dashi na damar mallakar manya-manya bayyanan sirri na hulda da kasashen wajen Amurka, domin biyan bukatar kanta, kuma ma'aikacin da duk yayi hakan har, aka gane shi to zai gane kuren sa.
Yanzu dai idan aka tabbatar da laifin da ake zargin ta da aikatawa zata fuskanci daurin shekaru 25 gidan yari.
Facebook Forum