Ba’a tantance yadda aikin sojojin Turkiya zai canja cikin Syria ba inda sojojin gwamnati da mayakan sa kan kungiyar ISIS da sojojin Kurdawa da kuma wasu kungiyoyin 'yan tawaye su ke gasar mallakar yankin.
A watan Augusta aka fara wannan aiki na fatattakar 'yan kungiyar ISIS.
Gwamnatin Turkiya ta na daukar mayakan Kurdawa a zaman wani bangare da 'yan kungiyar Kudistan Workers Party ko kuma PKK a takaice wadda ta share shekaru 30 ta na tawaye a kudu maso gabashin kasar ta Turkiya.
Amurka wadda take jagorancin sojojin taron dangi wadanda suke kai wa 'yan kungiyar ISIS hare-hare da jiragen saman yaki ta na goyon bayan mayakan Kurdawa, ta na daukar su a zaman mayakan da za su iya fatattakar 'yan ISIS daga yankin.
Facebook Forum