Tun jiya Laraba ake sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Amurka inda ya gana da Shugaban Amurka Donald Trump da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar. Sai har yanzu ba a ji labarinsa ba, lamarin da ya jawo damuwa da cece-kuce dangane da dalilin rashin dawowarsa.
Wasu na zargin ya tsaya domin duba lafiyarsa ne a birnin Landan, inda aka ce zai sake ziyarar duba lafiyarsa a wani lokaci a nan gaba.
Daga Landan, kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayyana cewa a karamin jirgi ne shugaban ya yi tafiya a cikinsa, don haka akwai bukatar ya huta kafin jirgin ya karasa tafiyarsa zuwa gida.
"Yanzu haka da muke magana da kai, ina tabbatar maka cewa shugaban ya bar Ingila a cikin jirginsa kuma yana kan hanya zuwa Najeriya. Muna sa ran wajen sallar isha'i na Najeriya zai isa gida." a yadda Garba Shehun ya shaidawa wakilinmu.
Saurari cikakken rohoton Umar Farouk Musa
Your browser doesn’t support HTML5