Shugaba Buhari Ya Yiwa 'Yan Najeriya Gaisuwar Sallah

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A cikin sakon gaisuwar sallah da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yi ya taya musulman kasar murnar kammala azumin wannan shekarar ta 2015 kamar yadda Ubangiji ya bada umurnin a yi.

Shugaba Buhari yace kodayake an kammala azumin wannan shekarar ya kamata a kiyayae da nasihar azumin kamar su sadakar da kai saboda bautawa kasa da yin kokari domin shawo kan kalubalen da suka durkusar da kasar.

Shugaban yace yanzu ya kamata a mayarda hankali wurin kawar da raunin da gurbatacen mulkin baya ya jawowa kasar domin a samu cigaba mutane kuma su ji dadin rayuwarsu.

Da yake duba baya yayi la'akari da yadda kasar ta yi watsi da damar da Allah ya bata na cigaba lamarin da ya sa wasu na cewa wannan lokacin shi ne dama na karshe da kasar ke dashi ta warware kanta daga kangin da ta shiga. Yin hakan kadai zai sa ta cimma muradunta da zama kasar da Allah ya nufeta dashi.

Shugaba Buhari yace fiye da kowane lokaci yanzu ne kasar take bukatan al'ummarta su sadakar da kai da nuna kishin kasa idan ana son kasar ta farfado da wuri daga raunin da ta samu saboda mugun mulki na rashin adalci da gaskiya da wawurar arzikin kasar

Allah ya ba kasar zarafi yanzu a yunkura a gyara kasar. "Mu tashi mu yaki tabarbarewar tsaro. Mu yaki cin hanci da rashawa da rashin cigaban kasa. Dole ne mu kuduri aniyar yin anfani da wannan damar mu hada kai mu yaki matsalolin da muke fuskanta. Mu yi kokari mu kawar da kowane irin kalubale saboda ci gaban kasarmu" inji shugaban.

Shugaba Buhari yace ashirye yake ya bada shugabanci na gari domin kawarda kurakuran da domin kasar ta kama hanyar zama kasa ta gari da zata anfani duk al'ummarta da albarkatun da Allah ya bata ba wasu 'yan tsiraru za'a bari su mamaye arzikin kasar ba, su kada daga su sai iyalansu da 'yan amshin shatansu, muggan mutane da babu ruwansu da rayuwar kasar.

Shugaba Buhari yace duk wani kokarin da zai yi na cigaban kasa da yakar mugayen dabi'u da aka saba yi a kasar sun ta'alaka ne akan irin goyon bayan da zai samu daga al'ummar kasar.

Saboda haka wajibi ne ya samu hadin kan kowa da kowa domin kawo karshen ukubar da al'ummar kasar ke sha. Yace al'ummar kasar su yadda dashi cewa ya kuduri aniyar kawo canji, canjin da zai ba kasar alkibla mai ma'ana da ba kowa 'yanci da walwala da damar cin anfanin kasar.

Daga karshe ya roki Allah ya bishe da al'ummarsa ya kuma albarkacesu