Makon da ya gabata ne aka sami tashin bom a kusa da masallacin da Sheikh Yahaya Jingir yake gudanar da tafsirin watan Ramadan, da ya yi sanadin rasa rayuwa da dama. Da kuma wani bom da aka sanya a ikilisiyar ECWA Tudunwada dake Jos fadar gwamnatin jihar Plato, wanda aka dace bai hallaka kowa ba.
A cewar shugaban majalisar malamai ta kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, salon da maharan ke bi suna da dama, domin haka yayi kira ga jama’a da suyi lura. Sheikh Jingir yace tabarbarcewar harkokin tsaro ya sa kungiyar Boko Haram yin barazana ga harkokin ilimi da take bin al’umma tana kashewa a makarantu, da Masallatai da Majami’u. Saboda haka ake bukatar dukan jama’a su ba gwamnati hadin kai domin shawo kan matsalar.
Yayi kira ga dukan al’ummar jihar Plato, har da wadanda basu gamaciji da juna, su hada kai domin kare rayukan al’umma.
A nashi bangaren mataimakin sakataren darikar ECWA na kasa Rev Eliza Baba cewa ya yi, a matsayinsu na shugabannin addinai, dam ace Allah ya basu ta fadakar da jama’a matakan da zasu bi wajen karfafa al’umma yadda za a zauna lafiya da juna.
Yace wannan lokaci ne da suka samu na ilimantar da al’umma, da hada kai da juna da kuma rayuwa tare. Yace hakin kowa ne ya sanar da hukuma idan yaga wani da bai amince da take takenshi ba, domin ganin an shawo kan duk wata fitina kafin ta tashi.
Ga cikakken rahoton.