Shugaba Buhari Ya Kira Gwamnoni Su Hada Karfi da Karfe Su Kawar da Cutar Shan Inna

Yaki da cutar polio ko shan inna a Najeriya

Yau Alhamis a Abuja shugaba Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta kawar da cutar shan inna kwatakwata daga doran kasar nan da shekarar 2017.

Shugaban ya kira duk 'yan Najeriya da su bada hadin kai wa gwamnatin tarayya domin cimma wannan manufar.

Yayinda yake ganawa da gwamnonin da cutar shan inna ko polio ta fi kamari a jihohinsu da wasu kungiyoyin dake fadakarwa akan yakar cutar Shugaba Buhari yace kafin kasar ta yiwa cutar adabo na har abada dole a dora akan nasarorin da aka samu da suka sa aka yi watanni 12 ba'a samu bullar cutar ba, wato tun daga watan Yunin bara zuwa watan Yulin wannan shekarar.

Shugaba Buhari yace ya kira taron ne da gwamnoni da kungiyoyi masu fafitikar kawar da cutar saboda bai kamata kasar ta sake komawa baya ba bayan an kwashi shekaru 17 ana yaki da kawar da cutar.

Shugaban yace ina son in sake jaddada cewa gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin cewa ta kare nasarorin da ta samu da yanzu zasu sa kasar ta kawar da cutar nan da zuwa shekarar 2017.

Ya cigaba da cewa saboda haka ina kira ku hada hannu da mu saboda kwararru sun yi mana kashedin cewa nasarar da muka samu tana tangatanga tana kuma tattare da hadarin maida hannun agogo baya idan ba mu yi taka tsantsan ba ko kuma muka yi sakaci.

Duk da cewa cikin shekara daya bamu samu bullar cutar ba a koina a kasar har yanzu akwai runa a kaba. Ina sane cewa idan muna son mu cigaba da zama kasa da bata da cutar dole mu kara kula ta yadda za'a ganota tun bata yi nisa ba koina a kasar kana a fadada tare da inganta bada allurar rigakafi.

Shugaban ya gargadi gwamnonin su sa ido akan yakin kawar da cutar a jihohinsu su kuma hada hannu da gwamnatin tarayya su tabbatar cewa sun baiwa shirin ayyukan aiki da suka dace da kuma yin aiki dasu ta hanyoyin da suka kamata.

Sjhugaban ya cigaba da cewa tsakanin yanzu zuwa shekarar 2017 dole mu tabbatar cewa mun cigaba da ba mutane kwarin gwiwar bada 'ya'yansu saboda a yi masu allurar rigakafi. Kazalika a dinga bin kananan hukumomi kain da nain domin a tabbatar cewa basu shiga yin barci ba wajen yaki da cutar.

Dole mu tabbatar babu cutar a kasarmu a shekarar 2017. Mu hada karfi da karfe domin cimma wanan muradun saboda 'ya'yanmu da zuri'ar da zata biyosu tare da tabbatar da lafiyar kasar gaba daya.

Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnonin goyon bayan gwamnatinsa tare da basu shugabanci nagari wajen kawar da cutar.

Wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya a Najeriya Dr Rui Gam Gaz ya yabawa kasar da irin gagarumin goyon baya da gwamnatin kasar ke bayarwa.

Ya gayawa shugaban Najeriya cewa daratsin da aka koya a Najeriya za'a yi anfani dashi wajen yin bincike kan yadda za'a dakile cutar polio a wasu sassan duniya.