Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa rundunonin sojin kasar wa'adi akan mukamansu.
Wani mukarrabin shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa karin wa'adin aikin, ya shafi babban hafsan hafsoshin sojan Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin; da babban hafsan rundunar sojojin kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai; da babban hafsan rundunar sojojin sama, Air Marshall Sadiq Abubakar; da kuma babban hafsan rundunar mayakan ruwa ta Najeriya, Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas.
Idan ba a manta ba, an fuskanci rashin sanin tabbas a bayan da wa'adoin hafsoshin ya cika a wannan wata na Disamba, bayan da suka samu karin wa'adin tun farko a watan Disambar bara. A bisa tsarin aikin na soja, wa'adinsu ya kamata ya kare a watan Yulin da ya shige ne.