WASHINGTON, DC - Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, a lokacin da ya ba mutane sama da 400 lambar yabo ta kasa, ciki har da Burna Boy, Teni, da 2Face, kamar yadda gidan talabijin din Channels na Najeriya ya bayyana.
Yayin da aka karrama Burna Boy da lambar yabon kasa ta MFR, wadda mahaifinsa ya taba samu, Teni da 2Face kuma sun samu lambar yabon MON, abin da Buhari ya ce sun cancanci samu.
“Wadanda suka cancanci a ambata sune mawakanmu, musamman Damini Ebunoluwa Ogulu (Burna Boy), wanda ya lashe lambar yabon Grammy a shekarar 2020," abinda Buhari ya bayyana kenan a wata sanarwa da hadimansa a fannin yada labarai Femi Adesina ya fidda.
“Burna Boy, tare da sauran mawaka, sun sake martaba masana’antar nishadi ta Najeriya a idon duniya a cewar sanarwar.
Bayan mawakan uku, sauran fitattun mutanen da suka samu lambar yabon sun hada da marigayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Darakta Janar din Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, da dai sauransu.
A sauran bangarorin kuma mutane 6 suka samu lambar yabon GCON, 55 suka karbi ta CFR, 65 suka samu ta CON, da dai sauransu.