Ganawa da shugaba Buhari yayi da mai bada shawara kan harkokin tsaro kanar Sambo Dasuki gabanin ziyarar aiki da zai kai a Nijar da Chadi daga gobe laraba, na daukar hankalin masana harkokin tsaro a Najeriya.
Babu wani cikakken bayanin ganawar ta asiri da baza ta rasa nasaba da harkar tsaro ba, musamman ma sabbin hare hare a jahar Borno da Yobe. ganawa da hafsoshin rundunonin soja da suka hada da janar Keneth Minima da Air Cheif Mashal Alex Bade da Air Mashal Adesola Amosu da Vice Admiral Jubril Usman.
Masana tsaro irin su Shinku mai ritaya na ganin zai yi wuya hafsoshin su dore kan kujerun su, a cewar shi "a matsayin su na shugabannin da aka ba alhakin gudanar da wasu abubuwa na tsaro, kuma an sami canjin gwamnati yanzu dan haka mautkar suna wannan wuri mai makon suyi kokarin gudanar da aikin yadda ya kamata, abubuwan da akayi ta korafi akai zasu yi ta kokarin rufawa.
Usman Usman na kungiyar fulani Nationwide a cewar shi duk wani garambawul da za'a yi ga harkokin tsaro a Najeriya zai fi tasiri idan ya shafi sashin 'yan sanda kamar yadda yayi kukan cewar baragurbi sun yin yawa a cikin su.
Sabon sufeton 'yan sanda Solomon Arase ya yi umurnin damke duk wani dansandan da ya zama dan koren 'yan siyasa ta hanyar rike masu jaka ko daga masu laima.
Ga El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5