Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya shaida wa sababbin Ministocinsa cewa, ‘yan Najeriya sun zaku su ga sauyi a rayuwarsu karkashin gwamnatinsa.
Tinubu ya shaidawa Ministocinsa hakan ne a lokacin da yake rantsar da su a farkon makonnan nan.
A jawabinsa kafin rantsar da ministocin, shugaban kasar ya ce, yana da kwarin gwiwa cewa, tare da gudummuwarsu, da mika wuya, gwamnati za ta iya zama abin dogaro.
Ba da jimawa ba da daukar rantsuwa, Shugaban kasar ya fara aiwatar da wadansu tsare-tsare da aka dade ana kai komo a kai a kasar da suka hada da soke tallafin man fetur da kwararru da dama ke bayyanawa a matsayin alheri ga kasar, lamarin da ya haifar da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kudaden waje.
'Yan Najeriya dai cike suke da burin ganin ministocin da aka nada sun kama aiki gadan-gdan tare da fito da tsare-tsare da za su saukaka rayuwar al'umar kasar.
Shugaba Tinubu ya yi fice a matsayin daya daga cikin tsoffin gwamnonin Najeriya da suka taka rawar gani da ayyukan da suka gudanar a jihohinsu wadanda suka zama abin misali.
Duk da ya ke bai yi farin jini ba lokacin yakin neman zabe, ana ganin matakan da ya fara dauka na iya banbanta gwamnatinsa, da ta magabacinsa Muhammadu Buhari duk da yake ya gaji kalubale da suka dabaibaye da ta shude.
Baya ga matsalolin tabarbarewar tattalin arziki, akwai sassan Najeriya musamman a arewaci da ke fama da kalubalen tsaro.
~ Hauwa Sheriff~