Shugaban hukumar zaben kasar Guinea ya sanar da shugaban kasar Alpha Conde a matsayin wanda ya sake lashe zabe domin wani wa’adin mulki na biyu, kwanaki shida bayan kamala babban zabe na kasa.
Conde ya sami kashi 58 cikin dari na kuri’un da aka kada, abinda ya hana zuwa zagaye na biyu a zaben da madugun hamayya Cellou Dlein Diallo yace an tafka magudu, ya sami kasha 31 bisa dari na kuri’un. Diallo yace damokaradiya ba a zaben. Ya kuma yi kira da a gudanar da zanga zanga domin nuna kin amincewa da sake zaben Conde.
Masu sa ido na kasa da kasa daga Kungiyar Tarayyar Turai sunce basu ga alamar magudi a zaben ba.
Conde ya kada Diallo a zaben fidda gwani da aka gudanar shekaru biyar da suka shige a zaben mulkin damokaradiya na farko da aka gudanar a kasar cikin shekaru da dama.