Shugaba Alpha Conde na kasar Guinea ya lashe zabe domin fara aiki wa'adi na biyu, kamar yadda hukumar zaben kasar tayi bayani, kwanaki shida bayan da aka zaben.
Shugaba Conde ya lashe zaben da kashi 58 cikin dari na kuri'a da aka kada.
Babban abokin takarar shugaba Conde Cellou Dalien Diallo, wanda ya sami kshi 31 cikin dari na kuri'u da aka kada yace anyi magudi. Jiya Asabar Diallo yayi alwashin cewa zai shirya zanga zanga kan abunda ya kira "fashi".
Masu sa ido kan zaben daga kungiyar tarayyar turai suka ce su dai basu ga magudi ba. Amma sunyi korafin kura-kurai ko matsaloli da suka gani da suka hada da jinkiri wajen bude rumfunan zabe,rijistar masu zabe suna hautsune, wadannan matsalolin biyu sun janyo dogayen layi na masu zabe.
Wannan shine kadai karo na biyu da za'a yi zabe bisa tsarin demokuradiyya Guinea tun bayan d a ta sami 'yancin kai daga hanun Faransa a shekara ta 1958.
Shugaba Conde ya zama shugaban kasa a shekara ta 2010 a zaben farko da aka yi a kasar, bayan shekaru masu yawa yana fafatawa da gwamnatocin kasar ta 'yan kama kariya, lamari da ya sa yayi gudun hijira.
A zaben kasar na farko da aka yi ya kada Diallo a zaben fidda gwani.