Shirin Zanga-Zanga: Gwamnoni Sun Bayyana Aniyar Tabbatar Da Tsaro A Jihohinsu

Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar bayan kammala taron kungiyar gwamnonin wanda aka soma a daren jiya Laraba aka kuma kammala da safiyar yau Alhamis a birnin Abuja.

Gabanin zanga-zangar tsadar rayuwar da matasan Najeriya ke shirin gudanarwa a watan Agusta, gwamnonin jihohin kasar 36 sun jaddada aniyar tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sanarwar bayan taron na dauke ne da sa hannun shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.

Gwamnonin karkashin inuwar kungiyar tasu sun ce ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro yayi bayani akan shirin zanga-zangar.

“Ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro ya yiwa kungiyar gwamnonin Najeriya bayani game da yanayin tsaro a Najeriya a halin yanzu. Inda mashawarcin shugaban kasar ya bayyana cewa akwai yunkurin da ake ci gaba da yi na gudanar da zanga-zanga dake bukatar gwamnati ta sa ido.

Abdulrazaq ya kara da cewa, kungiyar gwamnonin ta bayyana godiya ga mashawarcin shugaban kasar akan harkokin tsaro sannan ta jaddada aniyar inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a matakan jihohi.”