Shirin Zabe a Najeriya

  • VOA Hausa

Muhammadu Buhari

Wannan shafi ne na musamman da zai samar muku da labarai masu amfani da dumi-duminsu, game da muhimman zabubbukan da Najeriya zata gudanar a wannan shekara ta 2011. Wadannan labarai zasu hada da sauti, da bidiyo, da rubutattun bayanai daga kowane bangaren siyasa, babu sani ba sabo.
20/04/11

Muhammadu Buhari, CPC - Janar Buhari ya aza laifin tarzomar bayan zabe kan bata gari. Jam’iyyar CPC tana kira ga magoya bayanta kada su yar da da abinda ta kira wasu bata gari suna fakewa dasu suna barnar rayuka da dukiyoyin jama’a,da sunan bayyana rashin amincewar su da sakamakon zaben shugaban kasa.

1/04/11

Lauya Aminu Hassan Gamawa wanda ke yin digirin digirgir a jami'ar Harvard ta birnin Boston a jahar Massachussetts, ya ke bayani akan yadda manyan jami'an gwamnatin Amurka su ke ganin Najeriya, kuma ya yi amfani da damar da ya samu ya mika shawarwari ga 'yan uwan shi 'yan Najeriya wadanda ke shirin yin zabe. Halima Djimrao ce ta tattauna da Lauya Aminu Hassan Gamawa.

16/02/11

Ibrahim Shekarau, ANPP - A cikin wannan hira, Malam Ibrahim Shekarau, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ANPP a zaben 2011, yayi magana a kan batutuwa da dama ciki harda matakai da falalar shugabanci, da irin abubuwan da ake bukata ga shugaba da kuma wanda duk ke son zama shugaban jama'a, musamman a kasa kamar Najeriya.

16/02/11

Muhammadu Buhari, CPC - A cikin wannan hirar, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC, yayi magana a kan abubuwa kamar kokarin hada kai a tsakanin jam'iyyun hamayya da nufin takalar jam'iyyar PDP mai mulki, da kuma rikice-rikicen da suka dabaibaye jam'iyyar CPC a wasu jihohin kasar.

16/02/11

Nuhu Ribadu, ACN - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ACN, Malam Nuhu Ribadu, yayi magana a kan kokarin da suka yi na fito da dan takara guda wanda zai kalubalanci dan takarar jam'iyyar PDP, da kuma abubuwan dake ba shi kwarin guiwa a kan cewa su na iya kayar da jam'iyya mai mulkin a saboda irin abubuwan da suke gani kamar rauni a gare ta, da 'yan takararta.

08/02/11

Interview with Barrister Garba Pwul on extention of dateline for Voter registration execise.

15/12/10

Interview with INEC Chairman Prof Attahiru Jega.