Jam'iyyar ACN ta zargi abokan hamayyarta da laifin kulla mata makarkashiya a bayanda wani jirgin saman dake dauke da dan takarar mataimakin shugaban kasarta ya kara da dabbobi a filin jirgin saman Bauchi.
Jam'iyyar ta Action Congress ta ce talata ne jirgin dake dauke da Fola Adeola, mai yi mata takarar mataimakin shugaban kasa, ya kara da tumaki da awaki wadanda suka mamaye hanyar sauka da tashin jirage a filin jirgin saman.
Jam'iyyar ta ce tana kyautata zaton wata makarkashiya ce aka kulla, ta kuma nemi da a gudanar da bincike.
Ta ce dan takarar nata bai ji rauni ba, amma kuma jirgin ya lalace.
Har ila yau, jam'iyyar ACN ta ce jirgin saman dake dauke da dan takarar shugaban kasarta, Nuhu Ribadu, sai da ya shafe fiye da awa daya yana shawagi a sama kafin aka share hanyar saukar jiragen filin jirgin saman na Bauchi ya samu ya sauka.
Mutanen biyu sun je Bauchi ne domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar a can.
Najeriya zata gudanar da zabubbuka a watan Afrilu, amma a can baya, an fuskanci ayyuka na magudi a zabubbukan da aka gudanar a kasar.