A halin yanzu ‘yan kasuwar canjin na zaman dardar sakamokon samamen da jami’an hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya suka kai musu a cikin wannan makon, a wani mataki na dakile faduwar darajar naira da a yanzu haka ake canza dala daya kan naira 840, har ma 900 a wasu wuraren kuma ana hasashen ta kai 1,000 kafin karshen shekara.
Rahotanni sun yi nuni da cewa masu neman canza kudi daga naira zuwa dala su suka haddasa tashin farashin kudin don kaucewa zuwa banki, saboda yin hakan zai sa a gano makudan kudin da suka boye.
Wasu daga cikin masu harkar canji sun danganta hakan da karancin samun kudin dala daga babban bankin kasar da kuma matakin wa’adin da gwamnati ta bayar game da shirinta na canza launin kudin naira zuwa karshen shekarar 2022.
Babban bankin Najeriya na CBN ya ce wannan mataki na canza launin naira da gwamnati ke son yi zai taimaka wajen fitar da tsofaffin kudade da wasu marasa kishin kasar ke boyewa, da rage hauhawar farashin kayayyaki, yaki da matsalolin tsaro, da cin hanci da rashawa da kasar ke fuskanta. Sai dai talakawa na kokawa kan yadda hakan ke shafar al’amuran rayuwarsu na yau da kullum a cewar masanin tattalin arziki a Najeriya malam Sa’idu Salisu.
Duk da wannan matsi da ake ciki a yanzu sakamakon tashin dala a kasuwannin canji dole ne ‘yan Najeriya su kara yin hakuri, domin a cikin kankanin lokaci farashin dala zai sauka, in ji mai sharhi kan al’umuran yau da kullum Hassan Sardauna. Yana mai cewa matakin da gwamnatin kasar ta dauka zai taimaka wajen samun sauki a yanayin kunci da ake ciki a yanzu.
Tun dai a watan Yulin shekarar 2021 ne babban bankin kasar na CBN ya hana bada kudaden ketare ga kamfonin canji a fadin kasar bisa zarginsu da hannu wajen safarar haramtattun kudade, da damfara, da dai sauran miyagun laifuffuka.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5