Shirin Kawar da Barace-Barace a Jihar Bauchi

  • Ibrahim Garba

Wani nakasasshe bisa keken nakasassu

Nakasassun jihar Bauchi sun ce gwamnatin jihar ta dau matakan kau da bara da su ka hada da samar ma su da abinci da koya masu sana'o'i.
A wani yinkuri na rage barace-barace a jihar Bauchi gwamnatin jihar ta shiga raba kayan abinci da kuma samar da ayyukan yi ko kuma koyar da sana’o’i ma nakasassun a jihar. Wannan a cewar wakilinmu a Bauchi Abdulwahab Muhammad shi ne matakin farko na ragewa ko kuma kawar ba barace baracen kwata-kwata a jihar.

Sarkin Makafin Jihar Bauchi Abdullahi Jibir, wanda shi ne gwamna Isah Yuguda ya bai wa aikin raba kayan abincin, ya ce akwai masara da shinkafa da gero da kuma suga. Alhaji Jibir ya ce saboda irin wannnan tallafin da ake bayarwa har ma nakasassun jihar Bauchi sun daina yin bara in banda nakasassu baki da kuma wadanda ba su da godiyar Allah.

Shi kuwa Shugaban gamayyar kungiyoyin nakasassu a jihar Bauchi, Ali Abdullahi Shango, ya tabbatar cewa an ma dank wan biyu ana bayar da irin wadannan kayan tallafin. Ya kara da cewa lallai wannan matakin ya rage rawan barace-barace a fadin jihar. Ya kuma sauran matakan da aka dauka kuma sun fara taimaka ma nakasassu wajen dogaro da kai. Malam Shango ya kuma ce matar gwamna Isa Yaguda Abiodun Isa Yuguda ta samar da wuraren koyon sana’o’i ma nakasassun jihar.

Your browser doesn’t support HTML5

Shirin Kawar Da Bara A Jihar Bauchi