Kisan gillar da aka yiwa takwas cikin matasan wadanda daga baya an ce 'yan kungiyar masu yin haya da keken napep ne. Lamarin ya jawo cecekuce har majalisun kasar suka kafa kwamitocin bincike.
Majalisar dattawan Najeriya ta kafa tata kwamitin karkashin shugabancin Janaral Mohammed Magoro. Da ya gabatar da rahoton kwamitin nasa makon jiya sakamakon binciken nasu ya tayar da jijiyoyin wuya tsakanin dattawan da ma kungiyar 'yan keke napep.
Janaral Mohammed Magoro ya ce kwamiti daya suka kafa ba biyu ba. A duk zamansu da suka yi babu lokacin da suka gaza kasa da mutane 18 cikin su 20 da aka kafa. Lokacin da suka zauna sun tuntubi mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da hafsan hasoshin sojoji da daraktan din SSS da sifeto na 'yansanda har da ma kungiyar 'yan keke napep da lauyansu.
Gidajen da aka kai harin kowanensu ya kunshi mutane fiye da dari da hamsin. Wani Suleiman dake sana'ar keke napep dan kungiyar Boko Haram ne kuma shi ne yake jigilar 'yan kungiyar yana tarasu suna mitin suna shirya wuraren da zasu kai hari. Na'urar jami'an SSS dake sauraren maganar da mutane ke yi ta sa suka gano shirin da 'yan Boko Haram da suka labe da sana'ar keke napep ke yi na shirya hahe-hare.
Shi Suleiman ya ambaci duk sunayen 'yan Boko Haram da cikakken bayanin inda suka binne makamai.
Medina Dauda nada cikakken bayani.