Sai dai daga bisani gwamnatin ta daga wa'adin zuwa yau. Sakataren Hukumar Jami'o'in Njaeriya ko NUC a takaice Farfasa Julius Okoji shi ya sanarda da karin wa'adin wai domin kungiyar ta kammala jana'izar tsohon shugabanta da ya gamu da ajalinsa a wani hatsarin mota.
Yau sabon wa'adin ya cika kuma inji Farfasa Okoji kuma duk malamin da bai koma bakin aiki yau ba zai yi asarar albashinsa. Haka ma wani dan majalisar gudanar da Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi ya ce zasu sa ido su gani malamai nawa suka dawo kana su san matakin da zasu dauka nan gaba. Ya ce da malaman da gwamnati suna da 'yancin su kai kara a kotun sasantawa. Amma ya roki malaman da su kai zuciya nesa.
Amma duk baraznar da gwamnati ke yiwa malaman basu raunata ba. Suna nan kan bakansu, wato, babu gudu babu ja da baya sai sun ga abun da ya tubewa buzu nadi.
To sai dai wani mai sharhi kan siyasa kuma masanin tattalin arziki Aminu Kurfi ya ce matakin da gwamnati ta dauka bai dace ba. Ministan ilimin Najeriya yana abu kamar wani jahili. Ya kamata shugaban kasa ya sauya masa wurin aiki. Ya ce idan gwamnati ta kori malaman zasu samu aiki a kasashen waje su bar jami'o'in jida su zama fanko
Ga karin bayani.