Wannan tallafi dai yana daga cikin kasafin kudin bana, haka kuma mataimakin shugaban bai tsaya kan mata kadai ba harma da matasa wanda yace, suma gwamnati na shirin koya musu sana’o’I domin samun dogaro da kai.
Wannan tallafi dai da zai shafi mata da matasa da suka kai kimanin dubu 500, ba zai yi la’akari da takardun makaranta ko wani zurfin ilimi ba, ba kamar yadda Osinbajo ya ambaci bayar da Naira dubu biyar-biyarba duk wata ga talakawa a wani taro a jami’ar Ibadan bara, wanda daga baya hakan ya sami sauyin tunani, to wannan karo yayi wannan jawabi ne a Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan dai duk ya dogara ne kan amincewa da kasafin daga shugaba Buhari wanda daga alamu yake bita kan kasafin, inda ake gudun kar wani abu ya buya ko a cire wani sashe, wanda komai dai zai iya faruwa a ra’ayin masu sharshi ta amincewa ko mayar da kasafin majalisa don sake bita.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5