Sai dai masana sun danganta wannan matsalar da rikon sakainar kashin da shugabanni keyi wa wannan matsalar.
Wannan yasa ire-iren wadannan tashe-tashen hankulan sun mayar da wasu wurare tamkar kufai domin kama daga garin Jos ko BarikinLadi na jiharPilato, kudancin Kaduna har zuwa kudancin Taraba kusan fa zance guda ne na fadan kabilanci ko na addini.
Domin magance wannan ne cibiyar kawo fahintar juna tsakanin Musulmi da Kirista ta Inter Faith Mediation tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi gudanar tarurrukan sasantawa domin gano bakin zaren magance wannan matsalar.
A karshen wani rtaro da cibiyar ta gudanar a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya shugabanni n addin da kuma na al’umma sun bukaci gwamnatocin arewa ne dasu tashi tsaye.
Ga Ibrahim AbdulAzeez da ci gaban rahoton 3’06