Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata ‘Yan Jamiyyar APC A Jihar Bauchi Sun Koka


Women hold placards which read, "Bring back our girls", during a demonstration near the Eiffel Tower in Paris, May 13, 2014.
Women hold placards which read, "Bring back our girls", during a demonstration near the Eiffel Tower in Paris, May 13, 2014.

Bangaren mata ‘yan siyasa na jamiyyar APC kenan daga shiyyar katagun a jihar Bauchi ke bayyana takaicin su dangane da watsi dasu a bayan da aka kafa mulki a jihar Bauchi.

Ga dai abinda wasu daga cikin matan suka shaidawa Abdulwahab Mohammed.

‘’Nice Hajiya Hajara Ayuba daga karamar hukumar katagun, abinda ke tafe damu shine ansha wahala damu, munje munyi karairayi ga Jamaa sun fito sunyi zabe kuma daga karshe an zubar damu ba a ma neman shawarwarin mu ba a Magana damu balantana ahar a taimaka wa wadanda suka fito suka jefa kuria.’’

Sai dai Abdulwahab ya tambaye ta tana nufin wannan gwamnatin bata yi dasu? Ga kuma abinda ta shaidawa masa.

‘’Wallahi wannan gwamnatin bata yi damu saboda haka mu gwamnati bamu san abinda take yi ba, idan taro ne sai dai muji matar gwamna tazo anyi kaza da kaza tace zata taimaka sai dai muji wai a Radio idan har an tafi a haka to muna jiran shekaru hudu su dawo, idan shekara 4 tayi za a rabe da magirbin yakuwa idan mune masu jamaa za a gani, idan kuma shugabannin jamiyyar ce masu jamaa zasu gani.’’

Ga Abdulwahab Mohammed da Karin bayani 3’17

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG