Shin Wa Ya Fi Hazaka Tsakanin Mata Da Maza a Makaranta?

Shin da gaske ne maza sun fi mata kokari a wajen lissafi? Su kuma ‘yan mata sun fi maza kokari a wajen Ingilishi?

Wani bincike da aka gudanar a jami’ar Stanford, ya bayyana da cewar ana samun tazara tsakanin maza da mata ba mai yawa ba, haka kuma akwai wasu dalilai da ba su da alaka da jinsi, kamar arzikin gida da ilimin iyayen yaran.

Jami’ar ta gudanar da binciken akan sakamakon jarabawar dalibai milliyan 260, daga makarantu 10,000 a kasar Amurka, daga shekarar 2008 zuwa 2015, binciken ya gano cewar.

-Banbancin da ake samu a fannin lissafi a tsakanin maza da mata ya ragu a cikin ‘yan shekaru.

-Yara maza sun fi ‘ya'ya mata kokari a bangaren lissafi da kadan.

-Yara maza sun fi ‘ya'ya mata kokari a lissafi a makarantun ‘ya'yan masu hali da wasu makarantun birane.

-Amma ‘ya'ya mata sun fi yara maza kokari a lissafi a makarantun ‘yayan talakawa, amma da kadan.

-Amma ‘yan mata sukan ci jarabawar Ingilishi a kowane yanayin rayuwa, ko dai ‘yayan talakawa ko ‘yayan masu kudi.

A cewar matashiya Erin Fahle, wadda take gudanar da binciken yayin kammala karatun ta na digirin-digirgir, ta ce akwai matsalolin da aka dauka a cikin jama’a da ke nuna cewar ‘ya'yan talakawa ba su da kokari, wannan ba gaskiya ba ne, ta iya gano cewar hakan kawai canfi ne.

Hasali ma, ‘ya'yan talakawa sun fi kokari domin kuwa ba su zama inda ake da abubuwan zamani, da za su dauke ma yaran hankali, kamar wayoyin hannu, kwanfuta da dai sauran abubuwa makamantan haka.

Tana ganin cewar ‘yayan talakawa sai sun fi cin jarabawa ko dai ta lissafi ko ta Ingilishi, muddun an ba su da kwarin gwiwa da ya kamata.