A yau Alhamis ne kamfanin Google ya kaddamar da wasu cibiyoyi da za’a rika ba mutane damar amfani da yanar gizo kyauta. A wani yunkuri na kamfanin da yake don taimakama marasa karfi a kasashen Afrika.
Kamfanin ya fuskanci cewar taimakama matasa musamman ta hanayar samun yanar gizo cikin sauki zai taimaka wajen kara samu fahimtar me duniya take ciki. Kamfanin zaiyi aiki tare da wani kamfanin kasar Fiber Cable Network wajen wannan aikin.
Kamfanonin biyu sun zabi wasu cibiyoyi guda shida a birnin Lagos da suka hada ta tashar jirgi a jihar, ganin yadda yanar gizo keda karanci a kasar. Kimanin kashi 25.7 na mutane a kasar ne kadai ke amfani da yanar gizo.
Rashin yanar gizo mai nagarta na gurgunta harkar kasuwanci a kasar, wadda take uwa mabada mama a kasashen Afrika musamman idan akayi la’akari da yadda kasar keda arzikin man fetur.
A cewar mataimakain shugaban kamfanin Google Mr. Anjali Joshi, “mun fara wannan aikin ne a birnin Lagos, da niyar fadada shi zuwa ga sauran yankunan kasar. Kuma suna aiki tukuru don ganin an hada manyan garuruwa biyar da yanar gizo ta kyauta kamun nan da karshen shekarar 2019.
Facebook Forum